Libya

Gwamnatin Libya ta sanar da farmakin jiragen ketare kan sansanin Sojinta

Gwamnatin Libya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta ce wasu jiragen yaki na kasashen ketare sun kai hare-hare kan wani barikin sojinta da ke yammacin kasar.

Firaminista Fayez al Sarraj na Libya.
Firaminista Fayez al Sarraj na Libya. Drew Angerer/Getty Images/AFP
Talla

Gwamnatin ta Firaminista Fayez al Sarraj ba ta bayyana sunan kasar da take zargi da kai farmakin ba, duk da cewa ta na zargin Rasha da mara baya ga dakarun Haftar da ke rike da iko da yankunan gabashin kasar.

A jiya lahadi ne majiyar gwamnatin Libyan ta sanar da farmakin kan barikin soji na Al-watiya mai tazarar kilomita 140 daga Tripoli babban birnin kasar.

Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai dakarun gwamnatin mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya suka kwace iko da barikin daga hannun Khalifa Haftar mai samun goyon bayan Masar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Rasha.

Sanarwar farmakin na zuwa kwanaki kalilan bayan da Masar ta sanar da aniyar yiwuwar girke dakaru a kasar ta Libya bayan da gwamnati ta juya baya ga shirinta na sasanta rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI