Mali

Tsugune bata karewa shugaban kasar Mali ba

Wadanda ke jagorantar zanga-zangar adawa da shugaban Mali Ibrahim Bobacar Kieta, sun sha alwashin cigaba da matsin lambar tilasta masa yin murabus, sa’o’i bayan ganawarsu da shugaban a baya bayan nan.

Dubban masu zanga-zangar neman murabus din shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Kieta.
Dubban masu zanga-zangar neman murabus din shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Kieta. AFP Photo/MICHELE CATTANI
Talla

Ganawar ta karshen mako dai itace ta farko da aka yi tsakanin Ibrahim Boubacar Kieta da Mahmoud Dicko, malamin Islama kuma jagoran zanga-zangar neman murabus din shugaban na Mali.

Kieta dake shugabancin Mali tun daga shekarar 2013, ya kuma gana da wakilan jam’iyyun adawa da zummar yayyafa ruwa kan wutar rikicin siyasar dake barazanar yin awon gaba da gwamnatinsa.

Sai dai dai a jiya lahadi kawancen ‘yan adawar da ya kunshi shugabannin addini da na siyasa, ya sha alwashin cigaba da jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnati, saboda watsin da shugaba Kieta ya yi da bukatunsu, ciki har da rushe majalisar kasar nan take, da kuma kafa gwamnatin rikon kwaryar da su ne za su nada Fira Ministan ta.

An dai soma zanga-zangar neman kawo karshen shugabancin Ibrahim Boubacar Kieta ne ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata, inda dubban mutane suka fantsama a biranen Mali don nuna kosawarsu da gwamnati mai ci, da suka ce ta gaza magance matsalar hare-haren ta’addanci, da kuma rikicin kabilancin da ya raba karin dubban jama’a da muhallansu, musamman a yankin tsakiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI