Faransa

Ana zargin Ministan cikin gidan Faransa da aikata fyade

Sabon ministan cikin gidan Faransa Gérald Darmanin, da kama aiki ya hadu da zanga zangar kungiyoyi kare hakkin mata na Faransa da suka bukaci yayi murabus sakamakon zarginsa da aikata Fyade.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga dangane da nadin Darmanin a kujerar Ministan cikin gidan Faransa
Wasu daga cikin masu zanga-zanga dangane da nadin Darmanin a kujerar Ministan cikin gidan Faransa Thomas COEX / AFP
Talla

Zanga-zangar kungiyoyin matan na zuwa ne dai dai lokacin da sabon ministan cikin gidan Faransa Gérald Darmanin ke fara bisimilla a cikin aikinsa bayan da aka nada shi kan mukamin a ranar litinin da ta gabata.

A ranar talata ya kai ziyara a wata cibiyar yan sanda dake birnin paris inda daya daga cikin yan sanda biyu da aka kashe a gidansa a 2016, karkashin wani hari da wani mutum ya kai masa da kuma kungiyar ISIS ta dau alhakin kaiwa.

Zanga zangar farko kan ministan dai ta wakana ne a safiyar jiya talata a lokacin da yake karbar aiki daga tsohon ministan cikin gida Christphe Castener inda wani gungun mata sama da 20 suka kusanci shigen wayar ofishin ministan kafin jami’an tsaro su dakatar da su.

Masu zanga-zangar sun bukaci Darmanin da ya yi murabus ,suna dauke da alluna dake bayyana takaicinsu kan nadin da aka yi masa.

A marecen jiya kuma a bakin fadar shugaban kasar ta Elysée inda aka gudanar da taron majalisar ministocin gwamnatin Jean Castex na farko, wasu mata yan gwagwarmayar kare hakkin matan ne suka samu isa kusa ga fadar suna ihun neman murabus dinsa .

Dan lokaci kadan kuma wasu matan sama da hamsin sun taru a harabar mujami’ar Madeleine.

Idan dai ba a manta ba a 2018 wasu mata 2 suka zargi Gérald Darmanin da yi musu fyade da kuma nuna fin karfi, zarge zargen da ya musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI