'Yan Afrika miliyan 50 za su tsunduma cikin talauci- AFDB
Bankin Raya Kasashen Afrika AFDB, ya ce tasirin da annobar coronavirus ke ci gaba da yi kan tattalin arzikin duniya ka iya jefa karin mutane kusan miliyan 50 cikin mummunan talauci a nahiyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Sabon rahoton da bankin Afrikan ya fitar ya nuna cewa, kusan kashi 1 bisa 3 na yawan al’ummar nahiyar kwatankwacin mutane miliyan 425 aka bayyana cewa suna rayuwa kan kasa da Dala 2 a shekarar da muke ciki ta 2020, kuma yanayin ka iya munana nan gaba saboda tasirin annobar coronavirus.
Baya ga Oceania, Afrika ce nahiyar da ta fi samun saukin barnar annobar coronavirus a duniya, inda take da da kusan mutane dubu 500 da suka kamu da cutar, kuma daga cikin wannan adadin, kusan dubu 11 da 700 sun mutu, wasu akalla dubu 200 sun warke.
Sai dai matakan da gwamnatocin kasashen Afrikan suka dauke na killace jama’a da dakatar da ayyuka domin dakile yaduwar cutar, ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin nahiyar ta fuskokin asarar guraben ayyukan yi da kananan sana’o’i da kuma rasa makuden kudaden shiga a tsakanin kasashe masu arzikin danyen mai da sauran ma’adanai.
Wannan ce ta sanya bankin Raya Kasashen Afrika hasashen cewa, tsakanin mutane miliyan 28 zuwa miliyan 49 da dubu 200 ke fuskantar barazanar shiga tsananin talauci, sai kuma hasashen rasa guraben ayyukan yi kusan miliyan 30 a nahiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu