Burkina Faso-Amurka

Amurka ta yi barazanar katse tallafin tsaro ga Burkinafaso kan kisan fulani

Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafin da take bai wa Burkina Faso ta fannin tsaro sakamakon bayanan da ke cewa dakarun kasar na kashe fararen hula ba tare da an tabbatar da sun aikata wani laifi ba.

Wasu Fulani 'yan kabilar Gorom a Burkina Faso.
Wasu Fulani 'yan kabilar Gorom a Burkina Faso. Philippe ROY/Gamma-Rapho via Getty Images
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta sanar da gano wani makeken kabari dauke da gawarwakin mutane 180 a yankin Djibo da kuma Sahel da ke kasar ta Burkina Faso.

Benedicte Jeannerod, ita ce shugabar ofishin kungiyar ta Human Rights a Faransa, ta ce sun gano manyan kaburbura makare da gawarwakin mutane 180 dukkanninsu maza a yankin Jibo da ke arewacin kasar, batun da Amurka ke cewa matukar ya tabbata cewa kisan gilla aka yiwa fararen hular ko shakka babu za ta katse tallafin da ta ke baiwa kasar wajen yaki da ta'addanci.

A cewar jami’ar bincikensu ya tabbatar da cewa jami’an tsaron gwamnati na da hannu a kisan, domin bayanan da suka samu daga mazauna yankin na Jibo bayan gano gawarwaki, sun ce wadanda aka kashen dukanninsu Fulani ne, kuma kafin kashe su, sai da aka rufe masu fuskukoki, aka daure su sannan aka bude masu wuta.

Sai dai jami’ar hukumar ta Human Right Watch ta ce sun yi farin ciki game da yadda gwamnati ta bayyana aniyarta ta bayar da hadin kai domin binciken wannan lamari, yayinda ta bukaci gwamnatin kasar ta Burkinafaso kan ta tabbatar da hukunta masu hannu a kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI