Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta kashe Sojin Najeriya 37 a hanyar Damboa zuwa Maiduguri

Rahotanni a Najeriya sun bayyana yadda wani harin mayakan Boko Haram ya hallaka Sojin kasar 37 akan babbar hanyar Miduguri zuwa Damboa da ke jihar Borno mai fama da hare-haren ta’addanci.

Wasu Sojin Najeriya bayan kwace garin Damasak daga hannun Boko Haram a shekarar 2015.
Wasu Sojin Najeriya bayan kwace garin Damasak daga hannun Boko Haram a shekarar 2015. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Harin wanda ya faru tun a Talatar da ta gabata, a jiya Laraba ne rundunar Sojin Najeriyar ta tabbatar da faruwarsa ga manema labarai sai dai ta bayyana cewa Soji biyu kadai ne suka rasa rayukansu.

Cikin sanarwar da Manjo Janar John Enenche na ma’aikatar tsraon kasar ya fitar, ta ce suma bangaren dakarun Sojin sun kashe mayakan na Boko Haram 17 a farmakin wanda aka fafata tsakanin bangarorin biyu.

Haka zalika sanarwar ta ce galibin mayakan na Boko Haram da suka iya tsira a farmakin, sun gudu ne da mummunar raunin harbi a jikkunansu.

Wasu shaidu da ke bayyana yadda farmakin ya faru akan babbar hanyar, sun ce da misalin karfe 7 na daren Talata ne dakarun Sojin wadanda ke ran gadi akan hanyar ta Damboa zuwa Maiduguri suka ci karo da bataliya guda ta mayakan na Boko Haram da ke fake a kauyukan Limanti da Bulabulin da ke tsakanin Birnin na Maiduguri da Damboa.

Wata majiya ta shaidawa jaridun Najeriyar cewa, nan take mayakan na Boko Haram suka hallaka Soji 27 yayinda daga bisani aka gano gawar wasu mutum 10 ko da dai har yanzu ana ci gaba da laluben wasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI