Mali-Ta'addanci

Sabuwar zanga-zangar adawa da gwamnati ta sake barkewa a Mali

Rahotanni daga Mali sun bayyana yadda dubban masu zanga-zangar bukatar murabus din shugaba Ibrahim Boubacar Keita suka datse manyan titunan birnin Bamako a yammacin yau juma’a tare da kona tayoyi a farfajiyar majalisar dokikin kasar wadda suke ci gaba da yiwa ruwan dutsu a yanzu haka.

Wasu masu zanga-zanga gab da harabar majalisar dokokin Mali.
Wasu masu zanga-zanga gab da harabar majalisar dokokin Mali. RFI/Coralie Pierret
Talla

Dubban masu zanga-zangar wadanda suka hallaka a babban dandalin da ke tsakar birnin na Bamako na neman lallai shugaban kasar ya gaggauta sauka daga mulki ne, sakamakon tsanantar rikici da hare-haren ta’addanci baya ga koma bayan tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Wasu bayanan sun nuna tuni masu zanga-zangar suka karbe iko da babban gidan radiyo da talabijin na kasar, yayinda suka ci gaba da kone-kone a wasu sassan birnin na Bamako.

Zanga-zangar wadda wata sabuwar hadakar kungiyoyi masu adawa ta gwamnati ta kira, ita ce irinta ta 3 a cikin watanni 2 da Mali ke fuskanta dukkanninsu bisa bukata daya ta ganin lallai shugaba Keita ya ajje aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI