Wasanni-Kwallon kafa

Salomon Kalu ya kulla kwantragi da Botafogo a Brazil

Dan wasan Cote D’Ivoire Salomon Kalou maI shekaru 34 bayan share shekaru a turai, ya na taka leda a kungiyoyi da suka hada da Feyenoord dake Rotterdam, Hertha Berlin tareda yada gajeren zango a Chelsea dake Ingila da Lille a Faransa, dan wasan ya samu isa Botafogo kulob dake kasar Brazil musaman a birnin Rio de Janeiro.

Salomon Kalou dan wasan Cote D'Ivoire
Salomon Kalou dan wasan Cote D'Ivoire AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Dan wasan da ya taka leda da kungiyar kasar sa ta Cote D’Ivoire sau 97 tareda zura kwallaye 28 da wannan kungiya, ya kuma buga wasannin cin kofin Duniya kama daga shekara ta 2010 zuwa 2014 ,ya kulla sabon kwantragin ne da kungiyar Botafogo har zuwa shekara ta 2021.

Dan wasan na Cote D’Ivoire ne na biyu dan kasar waje da ya kulla irin wannan kwantragi da wannan kungiya dake Rio de Janeiro a Brazil da sunan dan wasa baya ga dan wasan kasar japan Keisuke Honda mai shekaru 34.

Yankin na Rio de Janeiro na daya daga cikin yankunan Brazil da suka soma wasannin kwallon kafa tun bayan dakatar da haka, sabili da annobar coronavirus a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI