Najeriya

Sarkin Fulani Kwara na neman agajin Gwamnatin Najeriya

Sarkin Fulanin jihar Kwara Alhaji Usman Adamu ya bayyana ta damuwa ganin ta yada ake ci gaba da kisan fulani a wannan jiha,lamarin da ya sa Sarkin fulani na yankin gayyato ilahirin shugabannin Fulani a garin Ilorin.

Alhaji Usman Adamu Sarkin Fulani jihar Kwara
Alhaji Usman Adamu Sarkin Fulani jihar Kwara RFI Hausa
Talla

Dangane da wannan tsokaci daga sarkin Fulanin jihar Kwara,Kwamishinan yan sanda na jihar Kwara CP Kayode Egbetokun ya  sanar da daukar matakan da suka dace don kawo karshen rikicin dake janyo asarar rayuka.

kazalika mai magana da sunan yan Sanda na jihar Ajayi Okesanmi ya bayyana cewa  Kwamishinan zai gana nan gaba da jami'an tsaro da nufin magance  wannan rikici da ya kuno kai bayan fada tsakanin yan sintiri na kabilun Nufawa da Fulani a kauyen Lata dake yankin Patigi a jihar ta kwara,rikicin da ya janyo mutuwar mutane bakwai da suka hada da yara kanana da mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI