Duniya-Coronavirus

Hukumar lafiya ta aike da jami'an ta China

Hukumar lafiya ta Duniya ta damu ganin ta yada ake ci gaba da samun karuwar mutane dake kamuwa da Covid 19,Hukumar ta ce mutanen da suka kamu da cutar coronavirus kan iya zarce wandada ake da su yanzu haka.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black / World Health Organization / AFP
Talla

Yayinda jami'an hukumar lafiya suka sauka kasar China,Babban jami’in Adhanom Ghebreyesus da babbar murya ya na mai bayyana cewa, cutar na yaduwa ne kamar wutar daji ,inda aka bayyana mutuwar mutane kusan 556.000 daga cikin mutane milyan 12.3 da suka kamu da ita.

Wata jami’ar hukumar lafiya ta Duniya Maria Van Kerkhove ta bayyana cewa ya zama wajibi kasashen Duniya su dau matakan da suka dace cikin gaggawa don kawo karshen yaduwar cutar a Duniya.

Amurka ke sahun gaba dangane da yawan mamata inda aka kiyasta cewa mutane 133.000 suka mutu daga cikin mutane milyan 3.18 da suka kamu, ajiya an sake samu wasu sabin mutanen 63.000 da suka kamu da kwayar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI