Afrika

Jam'iyyar MPP ta bayyana Shugaba Kabore a matsayin dan takarar ta

Jiya asabar Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore ya lashe zaben fidda gwanin Jam’iyya mai mulki ta MPP domin neman wa’adin shugabancin kasar na biyu.

Rock Marc Chrisitan Kaboré Shugaban kasar Burkina Faso
Rock Marc Chrisitan Kaboré Shugaban kasar Burkina Faso Johannes EISELE / AFP
Talla

Shugaba kabore da aka zaba a shekara ta 2015 ya samu goyan bayan ya’an jam’iyyar sa sama da dubu 5000 da suka halarci gaggarumin gangami da ya gudana a Ouagadougou.

Sai dai wasu daga cikin yan siyasar kasar na kalon sa a matsayin mutumen da ya gaza wajen shawo kan matsaloli da suka jibanci tsaro, musaman gazawar gwamnatinsa wajen shawo kan matsalar hare-haren ‘yan bindiga, da suka addabi dubban ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI