Duniya-Coronavirus

Kwararrun likitoci na ci gaba da gargadi don yakar coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump sanye da kyallen rufe baki da hanci
Shugaban Amurka Donald Trump sanye da kyallen rufe baki da hanci REUTERS/Tasos Katopodis

Akalla mutane milyan 12.580.980 aka gano cewa suna dauke kwayar cutar Covid 19 a cikin kasashe 196. Annobar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 561.000. Amurka ke sahun gaba dangane da mutane da suka rasa rayukan su bayan kamuwa da cutar, akala mutane 134.729 ne suka mutu daga cikin mutane milyan 3.242073 da suka kamu da cutar.

Talla

Shugaban Amurka a karo na farko ya bayyana sanye da kyallen rufe hanci da baki a jiya asabar a yayin wata ziyara da ya kai wani asibiti soji dake kauyen Washington.

Tun bayan bulluwar wannan cuta a kasar Shugaban ya yi watsi da duk wani zancen kare kai daga kamuwa da ita kamar dai yada likitoci suka bukaci a yi, yayinda ake cig aba da fuskantar karin yawan mutane dake kamuwa da ita a yankin Latino –Amurika.

A Brazil mutane dubu 71.000 ne suka mutu, a Chili mutane dubu 11.000 yayinda a Perou aka bayyana mutuwar mutane dubu 11.000.

Brazil a mataki na biyu inda ake da mutane milyan 1.839.850.

Kwararru a fannin lafiya na ci gaba da gargadi, Gargadin kwararrun na zuwa ne bayanda cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Afrika tace zuwa ranar 10 ga watan Yuli, jumillar mutane dubu 543 da 136 sun kamu da cutar coronavirus a nahiyar, dubu 265 da 810 daga cikinsu kuma sun warke, yayinda annobar ta halaka dubu 12 da 474.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.