Mali

Mali: An saki jiga-jigan 'yan adawar da aka tsare bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati

‘Yan adawa a Mali sun ce jami’an tsaron kasar saki shugabanninsu da suka kama, saboda jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Kieta.

Yadda masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita suka lalata titunan birnin Bamako. 10/7/2020.
Yadda masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita suka lalata titunan birnin Bamako. 10/7/2020. © REUTERS/Matthiew Rosier
Talla

Daya daga cikin lauyoyin ‘yan adawar Alifa Habib Kone, yace tun a ranar Juma’ar da ta gabata aka tsare jagororin nasu.

Tun bayan soma zanga-zangar neman tilastawa shugaba Kieta yin murabus a farkon watan Yuni, jami’an tsaron Mali sun kame jagororin ‘yan adawa akalla 20.

A daren ranar lahadin nan kawancen ‘yan adawa a Mali da ya kunshi shugabannin addini da ‘yan siyasa, yayi watsi da matakan neman sulhu da su da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Kieta ya dauka, don kawo karshen zanga-zanga hade da tarzomar kin jinin gwamnatinsa da dubban ‘yan kasar ke yi.

Wannan ya biyo bayan matakin shugaba Kieta na rusa kotun kundin tsarin mulkin Mali, da kuma alkawarta cika wasu sharudda da ‘yan adawar suka nema, sai dai cikin sanarwar da suka fitar, kawancen yace babu wani sharadi da suke bukatar shugaban na Mali ya cika face yin murabus nan take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI