Sudan

Al'ummar Sudan sun fara cin gajiyar tallafin rage radadin coronavirus

Gwamnatin Sudan ta fara rabawa al’ummar kasar marasa karfi kudade a karkashin wani shiri da kasashen duniya ke goyan baya domin rage radadi talaucin da su ke ciki sakamakon annobar coronavirus.

Wasu Mata a Sudan.
Wasu Mata a Sudan. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Kudaden tallafin na daga cikin Dala biliyan kusan 2 da kasashe masu bada agaji suka gabatar lokacin da Jamus ta kaddamar ad gidauniyar taimakawa kasar ta Sudan wadda kasashe 40 suka bada taimako.

Essam Abbas, Daraktan ma’aikatar kudin kasar ya ce shirin zai tallafa kashi 80 na al’ummar Sudan da ke zama cikin halin kuncin rayuwa.

Kafin coronavirus ta sake tagayyara al'ummar ta Sudan galibin yankunan karkara har ma da birane na fama da matsanancin talauci biyo bayan durkushewar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta karkashin mulkin hambararren shugaban kasar Omar al Bashir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI