Mali

Manyan kungiyoyin Duniya sun yi tir da zanga-zangar Mali

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen Turai da kungiyar kasashen Afirka ta AU da kuma ECOWAS sun bayyaan damuwa kan zanga zangar da ke gudana a Mali wadda ta kai ga kone kone da kuma kashe wasu daga cikin masu zanga zangar.

Dandazon masu zanga-zangar adawa da shugaba Bobacar Keita na Mali.
Dandazon masu zanga-zangar adawa da shugaba Bobacar Keita na Mali. REUTERS/Matthiew Rosier
Talla

Wakilan wadannan kungiyoyi na duniya a Bamako sun yi tir kan duk wani tashin hankalin da ake gani a kasar da kuma amfani da karfin da ya wuce kima daga jami’an tsaro, inda suka bukaci kai zuciya nesa da cigaba da tattaunawa domin warware rikicin siyasar kasar.

Hukumomin agaji a Bamako sun ce ya zuwa yanzu mutane 11 suka mutu, yayin da 124 suka samu raunuka daga ranar juma’a zuwa jiya sakamakon zanga zangar da ta juye zuwa arangama.

Sau 3 kenan cikin watanni 2 Mali na fuskantar kazamar zanga-zangar kin jinin gwamnati da ke neman murabus din shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita sakamakon tsanantar ayyukan ta'addanci da tabarbarewar tattalin arziki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI