Najeriya

Najeriya ta salami ma'aikatan NNPC 850 daga aiki

Katafaren Kamfanin man Najeriya na NNPC ya kori ma’aikatan sa 850 kuma akasarin su sun fito ne daga matatun man kasar da basa aiki yadda ya dace.

Cibiyar kamfanin (NNPC)  a Abuja dake Najeriya
Cibiyar kamfanin (NNPC) a Abuja dake Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Sakataren kungiyar manyan ma’aikatan man kasar na PENGASSAN, Lumumba Okugbawa yace ma’aikatan da aka sallama sun kunshi kwararru da wadanda ba kwararru ba, tare da wadanda ke taimakawa wajen tafiyar da matatun man.

Kamfanin man NNPC bai yi bayani kan korar ma’aikatan ba, sai dai a makwannin da suka gabata, shugaban sa Mele Kyari ya bayyana damuwa kan asarar da kamfanin keyi wajen rashin ingantaccen aikin da matatun man kasar keyi, abinda ya sa Najeriya ta dogara da kasashen ketare domin samarwa al’ummar kasar tacaccen man fetur.

A watan Mayun da ya gabata, kamfanin NNPC yace yana da ma’aikata sama da 6,600 dake karbar albashi daga lalitar sa.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka dogara da albarkatun man fetur domin samun kudaden shigar da take amfani da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI