ECOWAS ta nada Jonathan matsayin jakadanta don sasanta rikicin Mali
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a matsayin Jakada na musamman wanda zai sasanta rikicin kasar Mali.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Ikechukwu Eze ya rabawa manema labarai ta ce an nade tsohon shugaban ne domin tattaunawa da bangarorin da ke rikici a Mali da zummar sasanta su domin samar da zaman lafiya.
Ana bukatar Jakadan na musamman ya gana da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da kuma bangarorin 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula a ziyarar da zai kai kasar.
Jonathan ya godewa kungiyar da kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan goyan bayan da ya bashi wajen bashi jirgin saman gwamnati da kuma duk abinda yake bukata domin samun nasarar aikin dake gaban sa.
Kasar Mali ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan zaben 'yan Majalisu da aka yi wanda kotu ta soke nasarar da 'yan adawa su ka samu ta bai wa bangaren shugaban kasa, abinda ya haifar da mummunar zanga zanga da kuma kiran shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga kujerar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu