A yau shirin zai kai mu fagen tsere kekuna a jamhuriyar Niger, wasan da a can baya ya daga tutar kasar a yammacin Afirka, amma a yanzu Nijar ta zamayar kallo gaban kasashe irinsu Burkina Faso,Benin Cote D’ivoire da su Togo.Abdoulaye Issa ke jagorantar shirin na yau juma'a.
Sauran kashi-kashi
-
Wasanni 'Yan wasa bakaken fata na fuskantar wariya a Turai Shirin na wannan lokaci ya mayar da hankali ne, akan batun nuna wariyar launin fata da ‘yan wasa bakar fata ke fuskanta a nahiyar Turai.29/05/2023 09:55
-
Wasanni Bahaushiya Mace ta farko da ke horar da 'yan wasan kwallon kafa Maza Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya leka garin Mai Tsidau ne a Karamar hukumar Makodan Jihar Kano ta arewacin Najeriya, dan kawo muku yadda wata baiwar Allah mai suna Coach Fatima, wadda ta zamo mace daya tilo da ke horas da kungiyar kwallon kafa ta maza, wadda zancen nan da ake tuni labarinta ya karade kafafen sada zumunta a Najeriya.15/05/2023 09:59
-
Wasanni Halin da tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya ke ciki Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan halin kunci da wasu tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya da suka wakilci kasar a matakai daban-daban ke ciki.24/04/2023 10:00
-
Wasanni Duniyar Wasanni: Tarihin Mesut Ozil tsohon dan wasan Jamus Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya duba tarihin tsohon dan wasan tawagar kasar Jamus da ya yi murabus daga buga kwallon kafa a ‘yan kwanakin nan wato Mesut Ozil.10/04/2023 09:58
-
Wasanni Yadda ake ci gaba da fafata gasar Super League din kasar Niger Shirin "Duniyar Wassani" na wannan makon ya leka ne Jamhuriyar Nijar inda ake ci gaba da fafatawa a gasar lik din kasar.An kammala wasan zagaye na farko a gasar lik din Jamhuriyar Niger, da kungiyoyi 14 ke fafatawa a cikin ta.Gasar ta bana ta fuskanci tsaiko da dama ganin yadda a tsakayar ta aka tafi hutu don halartar gasar CHAN, sannan kuma aka sake bada hutu ga 'yan wasa bayan kammala gasar.13/03/2023 09:57