Nijar

Matsalar gurbatar muhalli a garin Agadas

Wasu daga cikin yankunan da ake zubar da shara
Wasu daga cikin yankunan da ake zubar da shara DR

Matsalar gurbatar muhalli da kuma yawaita shara a unguwanni da dama na garin Agadas ya tilastawa mazauna unguwanni da sharar ta yi wa illa tsara kansu don kawo karshen lamarin.

Talla

A karkashin wasu kwamitocin sa kai da mazauna unguwani suka kafa, an kaddamar da gangamin tsaftacewa da kuma kare muhalli.

Da jimawa kungiyoyi suka bayyana damuwa dangane da irin yada ake fuskantar matsallar gurbata muhali a garin na Agadas.

Banda Agadas ,birane da dama a Nijar suka fuskanci irin wadanan matsaloli,kamar dai yada zaku ji a rahoton Umar Sani daga Jihar Agadas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.