Wasanni

Real Madrid ta lashe la Liga

Shugaban Real Madrid Florentino Perez  ya bayyana farin cikin sa tareda girmama mai horar da kungiyar Zinedine Zidane, hakan na biyo bayan nasarar kungiyar Real Madrid a gaban Villareal da ci 2 da 1.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan lashe kofin La Liga
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan lashe kofin La Liga REUTERS/Sergio Perez
Talla

Shugaban ya ce masu kokarin shafawa Zinedine Zidane kashin kaji, su ci gaba, a nasu geffen burin su shine na ci gaba da lashe kofi.

Shugaban da babbar murya ya na mai bayyana cewa Kaftin din Kungiyar Sergio Ramos mai shekaru 34, a matsayin sa na Shugaban kungiyar ya na da yekinin a kungiyar Real Ramos zai yi ritaya saboda haka masu fadi magaganu marasa dadi, ya na mai fatan wannan nasara za ta kawo karshen haka.

Shugaban ya yabawa wasu yan wasan da suka hada da Karim Benzema, Thibaut Courtois ,Casemiro da Ramos,yan wasan da suka gabatar da dukullaliar kungiyar da ta tabbatar da ikon ta a gasar cin kofin la Liga ,karo na 34.

Yayinda Real Madrid ke sheke ayarta, dan wasan Barca Lionnel Messi a jiya alhamis ya bayyana takaicin sa ganin ta yada kungiyar sa Barcelona ke ci gaba da fama da fadi tashi.

Messi ya bayyana cewa muddin aka kasa kawo gyara ga tafiyar Barca ,to an kama hanyar da nan gaba zai yi wuya kungiyar ta sake samun nasarori kamar dai yada aka saba gani a baya.

Messi ya ce tabbas ,wannan korafi ya gabatar da shi zuwa magabatan kungiyar,wanda suka kasa magance haka a dan tsakanin nan.

Messi ya kuma nuna shakun sa ganin salon yada yan wasan Barca ke taka tamola , a cewar sa zai wuya su lashe kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI