Najeriya

Ana shirin sake bude makarantu masu zaman kansu a Najeriya bayan hutun corona

Wasu daliban firamare a wata makaranta birnin Abuja, Najeriya.
Wasu daliban firamare a wata makaranta birnin Abuja, Najeriya. UNICEF

Ma’aikatar ilimi a Najeriya ta baiwa masu makarantu har zuwa ranar 29 ga watan Yuli su cika ka’idojin da ta gindya musu na sake bude makarantu.

Talla

Wata sanarwa da ta samu sa hannun darakatan yada labarai na ma’aiktar ilimin Ben Bem Goong ta ruwaito karamin minister a ma’aikatar na cewa wannan yunkuri na cewa wannan mataki na zuwa ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da ma’aikatar lafiya, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa da sauransu.

A cewar sanarwar, ma’aikatar ilimin ta gana da hukumar shirya jarabawa ta WAEC, kuma ta amince ta tuntubi wasu kasashe 4 a game da sauyin lokacin jarabawa.

Ma’aikatar ilimin ta ce kafin a bude makarantu dole sai ma’aikatun ilimi na jihohi sun gana da ma’aikatar ilimi ta kasa, tare da tattaunawa da kwamitin da shugaban kasar ya nada don yaki da cutar coronavirus da saura masu ruwa da tsaki, da zummar yin nazari kan abubuwan da ake bukata, wadanda aka jera a ka’idojin sake bude makarantun.

Bugu da kari, a kowace jiha, dole ne a samar da wani shirin kula da lafiya a makarantu, a karkashin jagorancin wani jami’i a jihar, yayin da kowace makaranta za ta nada jami’in da zai rika hulda da babban jami’in a matakin jiha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.