Cutar Ebola ta sake barkewa a DR Congo
Jami’an lafiya a Jamhuriyar Congo, sun ce annobar Ebola ta sake barkewa a arewa maso gabashin kasar, makwanni kalilan bayan da gwamnati ta yi shelar kawo karshen cutar, da ta lakume rayukan sama da mutane dubu 2.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar lafiyar Jamhuriyar ta Congo, ta ce daga farkon watan Yunin da ya gabata zuwa yau, an samu mutane 54 da suka kamu da cutar ta Ebola, gami da mutuwar wasu 22 a yankin Mbandaka.
Hukumar Lafiya ta duniya ta bayyana barkewar cutar Ebola ta baya bayan nan a matsayin wani abin damuwa, inda ta a Alhamis din wanna mko t gano mutane 58 da suka harbu da cutar.
Annobar na yaduwa ne a daga garin Mbandaka zuwa kauyukan da ke kewaye da shi a kusa d kogin Congo, wasu dga cikin su sai da kwale kwale ake iya zuwa ko kuma babur.
Wannan dai shi ne karo na 11 da cutar ke barkewa a kasar ta Congo, tun bayan soma bulla cikinta a shekarar 1976.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu