Covid19: Madagasacar ta nemi agajin kasashen Duniya

A wata wasika da ya aika wa cibiyoyin kiwon lafiya na kasa da kasa, ministan kiwon lafiya a kasar Madagascar Pr Ahmad Ahmad, ya bayyana matukar damuwa a game da yadda ake samun yawaitar masu kamuwa da cutar Covid-19 a kasar.A wannan wasika, ministan ya bayyana cewa kasar na bukatar tallafin kayan yaki da cutar wadda ta kama mutane dubu 7 da 548 tare da kashe mutane 65 a kasar.

Jami'an kiwon lafiya a kasar Madagsacar
Jami'an kiwon lafiya a kasar Madagsacar RIJASOLO / AFP
Talla

Duk da cewa an yi ta ne a asirce, amma nan take wasikar ta karede duniya sakamakon yada ta da aka yi a shafukan sada zumunta kafin daga bisani a fara karanta wasikar a labaran yamma na gidan talabijin mallakin gwamnatin kasar.

To sai dai bayanan da ke kunshe a wannan wasika sun yi hannun riga da na shugaban kasar Andry Rajoelina, domin kuwa wasikar ta fito fili karara inda ta bayyana cewa akwai dimbin mutane da ke kamuwa da wannan annoba ciki har da jami’an kiwon lafiya.

Ministan kiwon lafiya farfesa Ahmad Ahmad, a cikin wannan wasika, ya ce ana bukatar na’urorin taimakawa marasa lafiya numfashi guda 337, da kwalaben ajiye iskar gaz guda 1200 da kuma kyallayen rufe baki da hanci guda milyan daya.

Yayin da shugaban kasar Andry Rajeolina ke cewa an samu maganin warkar da cutar mai suna covid-organics, amma a nasa bangare ministan lafiya na cewa kasar na bukatar kwayoyin hydroxychloroquine dubu 328 000 a cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI