Afrika-Belgium

Iyalan Lumumba sun aike da wasika ga Sarkin Belgium

Shekaru 60 bayan kisan Patrice Lumumba, yar sa ta aike da wasika ga Sarkin Belgium don ganin an dawo da sauren kasusuwan mahaifin su.A jiya talata ne wasikar ta isa fadar sarkin Belgium.

Lokacin da aka kama marigayi Patrice Lumumba tsohon Firaministan kasar Congo
Lokacin da aka kama marigayi Patrice Lumumba tsohon Firaministan kasar Congo AFP PHOTO / STRINGER STRINGER
Talla

A wannan wasika iyalan Lumumba sun bukaci a dawo da gawar mahaifin su dake Belgium ,don ba su damar gudanar da zana’izzar mahaifin su cikin adalci kamar yada ta kamata.

Sauren kasusuwan sa na ajiye ne a fadar sarkin Belgium yanzu haka,a cewar yar sa, suna da tabbacin haka, sabili da akwai wani mutum a lokaci da ya bayyana a talabijen da cewa ya na rike da hakoran Lumumba biyu, mutumen na daga cikin mutanen da suka cin zarrafin sa.

A cewar Juliana Amato Lumumba yar marigayi Patrice Lumumba, sun samu wadanan bayyanai dake nuna cewa sauren kasusuwan Lumuba na ajiye ne a fadar Sarki Philippe na Belgium.

A gani Juliana Amato Lumumba suna daf da kawo karshen wannan dambarwa, a matsayin su na ya’an marigari, da jimawa suka samu kan su a wannan tafiya ta girmama mahaifin su tareda yi masa abin da ya kamata.

Lumunba da magoya bayan sa sun mutu sabili da kasar nan ,sun zubar da jinnin su sabili da wannan kasa a cewar Juliana Amato Lumumba, yi musu adalci shine na dawo da kasusuwan su gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI