Mali-Ecowas

Tawagar shugabanin kasashen Ecowas a tattaunawar Mali

‘Yan adawa a Mali sun sanar da dakatar da zanga-zangar adawa da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a daidai lokacin da ake dakon isar tawagar shugabannin kasashen yammacin Afirka 5 gobe alhamis a birnin Bamako don sulhunta rikicin kasar.

Zanga-zangar yan adawa a kasar Mali
Zanga-zangar yan adawa a kasar Mali MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Shugabannin kasashen Najeriya, Cote d’Ivoire, Ghana, Senegal da kuma Nijar ne za su ziyarci kasar ta Mali bayan da tawagar kungiyar Ecowas-Cedeao karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gana da bangarorin siyasar a cikin makon da ya gabata.

Ministan yada labaran Jamhuriyar Nijar Mahamadou Salissou Habi, ya bayyana mana kokarin da Ecowas ke yi don warware wannan rikici.

Tawagar shugabanin kasashen Ecowas a tattaunawar Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI