Afrika-Turkiya

Turkiya ta kulla yarjejeniya da wasu kasashen Afrika

Ministan harakokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu na gudanar da ziyarar aiki a kasashen Afirka da suka hada da Nijar, Equatorial Guinea da kuma Togo tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama da wadannan kasashe.

Recep Tayyip Erdogan Shugaban kasar Turkiya
Recep Tayyip Erdogan Shugaban kasar Turkiya Presidential Press Office/Handout via REUTERS
Talla

Wannan ne dai karo na farko da wani babban jami’in Turkiya ya ziyarci kasar Togo tare da kulla yarjeniyoyi har guda uku, da suka hada sanar da bude ofishin jakadancin Turkiya a kasar, da kuma fara zirga-zirgar jiragen saman kamfanin Turkish Airlines daga Lome zuwa kasar nan ba da jimawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI