Mali-Afrika

Shugabannin Afrika sun isa Mali don magance rikicin kasar

Shugabannin kasashen Afrika sun hallara a birnin Bamako da zummar lalubo hanyar magance rikicin siyasar Mali.

Shugabannin kasashen ECOWAS tare da takwaransu na Mali, Ibrahim Boubacar Keita
Shugabannin kasashen ECOWAS tare da takwaransu na Mali, Ibrahim Boubacar Keita Facebook/Femi Adesina
Talla

Shugabannin kasashen da suka hada da na Senegal da Ivory Coast da Ghana da Najeriya da kuma Nijar, sun tsara zaman ganawa da takwaransu na Mali, Ibrahim Boubacar Keita da kuma shugabannin ‘yan adawar da ke bukatar sa da ya yi murabus.

Rikicin siyasar Mali na ci wa makwabtanta tuwo a kwarya, lura da dari-darin cewa, kasar wadda ta gamu da musibar mayakan jihadi, ka iya tsunduma cikin mummunan tashin hankali.

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast da Macky Sall na Senegal, suka fara isa filin jiragen saman Bamako, inda shugaba Keita da kansa ya tarbe su, yayin da rahotanni ke cewa, an samu wata karamar tawagar masu zanga-zangar da suka yi dandazo a harbar filin jiragen saman.

Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Yahya Sylla ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, sun hallara ne domin neman murabus din shugaba Keita tare da tabbatar da an karrama abokan gwagwarmayarsu da aka kashe a kasar.

Tun a ranar 5 ga watan Yuni aka fara zanga-zangar bayan al’umma sun fusata kan gazawar shugaban wajen magance matsalar tattalin arziki da cin hanci da rashawa da kuma rikicin shekaru takwas na mayakan jihadi.

Kazalika mutanen Mali sun harzuka saboda sakamakon zaben watannin Maris da Afrilu da ya bai wa jam’iyyar Keita nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI