A cikin shirin 'Al'adunmu Na Gado' na wannan mako, Mohammane Salissou Hamissou ya yi nazari ne kan asalin masarautun gargajiya a Najeriya.
Sauran kashi-kashi
-
Al'adun Gargajiya Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan makon ya tattauna ne da kungiyar Gwape a jihar Neja Shirin Al'adunmu Na Gado na wannan makon ya tattauna ne da kungiyar Gwape a jihar Neja dake arewa maso tsakkiyar Najeriya, kungiyar da ke raya al'adun gargajiya na mutan wannan yanki.26/05/2023 09:55
-
Al'adun Gargajiya Mabanbantan abincin gado a kasashen Afrika Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yi nazari kan mabanbantan nau'ukan abinci da ake ci a wasu kasashen Afrika ta yamma kamar Ghana, Najeriya da Nijar.09/05/2023 09:56
-
Al'adun Gargajiya Ala'adar taimaka wa juna a tsakanin Hausawa da sauran kabilu a Togo lokacin Ramadan Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya mayar da hankali ne a kan tanade-tanaden al'adun Bahaushe, wadanda akasarinsu suka rungumi addinin Musulunci a game da tamakekeniya a lokacin azumin watan Ramadan. Shirin ya leka kasar Togo, inda ya tattauna da Hausa da ke zaune a wannan kasa tare da wasu kabbilu a game da hakan.28/03/2023 10:19
-
Al'adun Gargajiya Yadda wasan Tabastaka ke taka rawa a fannin zaman lafiya a Nijar Shirin "Al'adunmu na Gado" a wannan makon ya yi duba ne akan yadda wasan gargajiya na Tabastaka ke ta ka rawa wajen abinda ya shafi zaman lafiya a yankunan Damagaram da kuma Zindar.Haka nan kuma, shirin ya duba yadda al'ummar Hausawa suka rungumi abincin al'adar al'ummar kasar Ghana.Shirin bai tsaya nan ba sai da ya leka tarayyar Najeriya, inda ya kawo yadda aka gudanar da bikin nadin sabon Sarkin Kwantagora a jahar Niger da ke tsakiyar kasar.07/03/2023 09:56
-
Al'adun Gargajiya An yi bikin nadin sarautar Sarkin Dogarawa na garin Tahoua Shirin Al'adunmu na gargajiya a wannan makon ya tattauna akan bikin nadin sarautar garin Dogarawa da ke jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar.21/02/2023 10:08