Dubun matashi mai kudin tsafi ya cika

Hoton bidiyon wani matashi dan kasar Kamaru dake yawo kwanan nan a kafafen sada zumuntan intanet ya tada hankalin ‘yan kasar da kasashen ketare.

Wasu kayayyakin tsafi a yankin Zamfara na Nigeria
Wasu kayayyakin tsafi a yankin Zamfara na Nigeria buzzgh
Talla

Hoton bidiyon ya nuna matashin mai kimanin shekaru 25, mai suna Leonel Tchaps yayi tsirara bayan fitowarsa daga wani kanti a babban birnin kasar Yaounde, inda yayi siyayya.

Rahotanni dai, kamar yadda jaridun kasar da wasu muhara da yanzu haka gidajen talabijin din kasar kamarsu Equinox TV suka yada, na nuna cewa, matashin wanda dalibin jami’a ne a Yaounde, ya haukace ne, sakamakon rashin cika ka’idojin wani boka inda ya karbi jakar sanya kudi, ta Magic Wallet, wanda aka ce tana ninka duk irin kudin da aka sanya a cikin ta.(akace tana buga kimanin Cefa miliyan 5 kowace rana.

Dama dai shi wannan matashi ya yi kaurin suna wajen fachaka da kudade, wanda shi da kansa ke wallafasu a shafukansa na sada zumunta, yadda yake walwala da motoci da kayayyaki na katsaita, hatta kudin ma, ana ganin yadda yake ta watsar da su.

Rahotanni sunce, kafin haukacewar Tchaps da akewa lakabi da colonisateur, (masu mulkin mallaka) sai da abokansa biyar da ake ganinsu tare suna chasu suka rika mutuwa daya bayan daya.

Yanzu haka dai ana ta jimamin makomar yaron da kuma, jiran matakai da gwamnati zata dauka kan irin wadan nan matasa da bokayen da ke taimaka musu.

Don abaya bayan nan masu bada irin wannan jaka, har talla sukeyi da lambobinsu ta shafukan sada zumunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI