Ebola-Congo

'Yan bindiga sun kashe soji 1 da fararen hula 7 a DR Congo

Fararen hula 7 da kuma soji daya ne suka rasa rayukansu, a hare-hare biyu mabambanta da ake zargi mayakan kungiyar ‘yan tawaye ta ADF da kai wa a lardin Beni a gabashin jamhuriyar dimokuradiyyar Congo.

Félix Tshisékédi shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Félix Tshisékédi shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Tchandrou Nitanga / AFP
Talla

Wani jami’in gwamnati a yankin da lamarin ya faru mai suna Muhindo Isaya, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari na farko ne a wani kauye mai suna Kainama, yayin da suka kai hari na biyu a Ruwenzori duk a ranar jiya laraba.

Mataimakin gwamnan lardin Arewacin Kivu Didi Mouhindo, tabbas ‘yan tawayen ADF sun yi kutse a cikin kauyen Muhindo, kuma sun gano gawarwakin mutane 6 da suka hada da mata biyu da kuma maza masu manyan shekaru su 4.

Ya kara da cewa , maharan sun kona illahirin kauyen kurmus, sannan akwai mutanen da suka bata har yanzu babu labarinsu, ko kuma ma inda suke.

Sai dai ya ba da tabbac in cewa sojoji na iya kokarinsu domin tabbatar da tsaro da kuma kare lafiyar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI