Mali

Jagoran 'yan adawa ya sassauta matsaya kan tilastawa shugaban Mali yin murabus

Mahmoud Dicko, Malamin da ya soma jagorantar zanga-zangarneman tilastawa shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita yin murabus.
Mahmoud Dicko, Malamin da ya soma jagorantar zanga-zangarneman tilastawa shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita yin murabus. REUTERS/Matthieu Rosier

Malamin da ake kallo a matsayin jagoran zanga zangar adawa da shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, Mahmoud Dicko, yace za a iya warware rikicin siyasar kasar ba tare da tilastawa shugaban yin murabus ba.

Talla

Akalla mutane 14 suka rasa rayukansu a farkon wannan wata na Yuli, yayin zanga zangar ta neman rusa gwamnatin Kieta da aka soma tun cikin watan Yuni, yanayin da ya haifar da fargabar fuskantar koma baya a yakin da gwamnatin ta Mali ke yi da ‘yan ta’adda.

Tuni dai gamayyar ‘yan adawar Mali da suka kunshi ‘yan siyasa da jagororin addini suka yi watsi da jerin tayin sulhun shugaba Kieta da kuma na kungiyar ECOWAS mai shiga tsakani, inda suka nanata matsayarsu ta neman shugaban yayi murabus.

Sai dai sa’o’I bayan hakan, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Mahmoud Dicko ya sassauta matsayar neman tilasta murabus din shugaban na Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI