Bakin Haure

Sojin ruwan Tunisia sun ceto bakin haure har da jariri a teku

Wasu bakin hauren Tunisia da aka ceto a shekarar 2012.
Wasu bakin hauren Tunisia da aka ceto a shekarar 2012. Reuters/Coast guard Press Office/Handout

Sojin ruwan Tunisia a jiya Juma’a sun ceto wasu bakin haure 70 da kwale kwalen robar da suke ciki ke daf da nutsewa a teku, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Italiya daga Libya, kamar yadda ma’aikatar tsaro kasar ta Tunisia ta sanar.

Talla

Kakakin ma’aikatar tsaron Mohamed Zekri ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa kwale kwalen ya samu matsala ne a tsakiyar ruwa, kuma ya fara nutsewa kenan sojojin ruwanta suka kai dauki.

Mata 5 da yara 4, ciki har da wani jariri mai wata daya na daga cikin wadanda aka ceto daga wannan kwale kwale mai nutsewa, a cewar kungiyar agaji ta Red Crescent.

Bakin hauren sun da suka taso daga yammacin Libya a ranar Laraba, an grzaya da su tashar jiragen ruwa na Zarzis a kusa da iyakar Libya a kudancin Tunisia.

Gwamnatin Italiya taa ce kusan rabin bakin haure dubu 11 da suka isa gabar ruwanta ‘yan Tunisia ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI