Najeriya

Wasu daga jami'ai na sun ci amanar da na ba su - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce wasu daga cikin jami’an da ya baiwa shugabancin hukumomin kasar sun ci amanar da ya basu.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja, bayan gudanar da Sallar idi a jiya Juma’a, inda ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yiwa shugabanni da manyan jami’an wasu daga cikin hukumomin gwamnatinsa da suka hada da NDDC da kuma EFCC.

Karo na farko kenan da shugaban Najeriyar yayi tsokaci kan binciken almundahanar makudan kudade da kadarorin da aka bankado a hukumar raya yankin Niger Delta NDDC dake karkashin tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio, da kuma hukumar yakar rashawa EFCC da aka dakatar da mukaddashin shugabanta Ibrahim Magu, da aka zarga da karkatar da makudan kudaden da satar da aka kwato, zargin da yake ci gaba da musantawa.

Har yanzu kwamitin binciken da gwamnatin najeriya ta kafa a karkashin Ayo salami tsohon shugaban kotun daukaka kara ta Najeriya na ci gaba da aikin gano gaskiyar tuhume-tuhumen da ake yi wa Magu.

A baya bayan nan aka bankado bacewar kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 40 a hukumar NDDC, abinda ya sanya shugaba Buhari kafa kwamitin da zai binciki yadda aka tafiyar da hukumar ta NDDc tun daga shekarar 2001 zuwa 2019.

Tuni dai kwamitin majalisar dokokin Najeriya ya soma gudanar da bincike kan badakalar ta NDDC, abinda a kwanakin da suka gaba ya tayar da kura, bayan da shugaban hukumar Godswill Akpabio ya wallafa sunayen wasu ‘yan majalisar dokokin Najeriyar da yace suna baiwa kwangiloli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI