NAJERIYA -BANDITS

Dakarun Najeriya sun kashe 'yan bindiga 80

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce sojin kasar sun halaka ‘yan bindiga 80 tare da ceto mutane 17 da suka yi garkuwa da su.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar yau asabar, mai’aikatar tsaron ta ce dakarun Najeriyar sun samu nasarar ce bayan kaddamar da samame kan gungun ‘yan bindigar a Katsina, Zamfara da kuma Sokoto, daga 1 zuwa 31 ga watan Yulin da ya kare.

A tsawon watan guda da suka shafe suna yakar ‘yan bindigar, sojin Najeriya sun kuma yi nasarar kwato shanu 943 da maharan suka sace, tarin makamai da kuma kame mutane 14 dake taimakawa ‘yan bindigar da bayanan leken asiri.

Kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya yace komawar manoma zuwa gonakinsu a wasu sassan da a baya ke fuskantar barzanar ‘yan bindiga, shaida ce ta nasarorin da suka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI