Kamaru

Mayakan Boko Haram sun halaka mutane 13 a arewacin Kamaru

Jami'an tsaron Kamaru yayin sintiri a wajen yankin Mosogo dake yankin kasar na arewa mai nisa
Jami'an tsaron Kamaru yayin sintiri a wajen yankin Mosogo dake yankin kasar na arewa mai nisa AFP

Majiyoyi daga hukumomin tsaron Kamaru sun ce mayakan Boko Haram sun halaka akalla mutane 13 tare da jikkata wasu 8, Yayin farmakin da suka kai da bama baman gurneti kan kauyen geshewa a arewacin kasar.

Talla

Magajin garin Mozogo inda aka kai farmakin, a yankin na arewa mai nisa, Medjeweh Boukar, yace gungun mayakan na Boko Haram da ba a tantance yawansu ba sun farwa wani sansanin yan gudun hijira dake kauyen Geshewe a gaf da iyakar Najeriya inda suka jefa bama baman gurneti cikin taron jama’a.

Sai dai daga bisani wani jami’in tsaro ya ce adadin rayukan da suka salwanta a farmakin ya karu zuwa 15, bayan mutuwar biyu daga cikin mutanen da suka jikkata.

Cikin watan yunin shekarar bara, kimanin mayakan Boko Haram 300 suka afkawa wani tsibiri a zagayen Tafkin Chadi dake yankin arewa mai nisa a Kamaru, inda suka kashe mutane 24 ciki har da sojoji 16 dake shingayen bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI