Harin ta'addanci ya hallaka sojojin Mali 5

Akalla sojin Mali 5 suka mutu a lahadin nan bayan da mayakan jihadi suka kai musu tagwaye hare hare a yankin tsakiyar kasar, lamarin dake zuwa a daidai lokacin da ake cigaba da rikicin siyasa, wanda tuni ya janyo Kasashe tsoma baki dan sasantawa.

Sojojin Mali a yankin Gao na kasar
Sojojin Mali a yankin Gao na kasar Souleymane Ag Anara / AFP
Talla

Majiyar tsaro ta bayyana harin kwantan baunar da mayakan jihadin suka kaiwa tawagar sojin Kasar da kuma sansanin su dake tsakiyar Mali ya yi sanadiyar kashe sojoji 5, wasu 5 kuma suka jikkata.

Kazamin harin na zuwa ne makonni 6 bayan wani harin kwantan bauna da mayakan suka kaiwa wata tawaga ta daban, kuma a tsakiyar Mali, harin da ya yi sanadiyar mutuwar dakarun tsaron kasar 24.

Ko a shekarar 2012 mayakan jihadi sun ci Karen su babu babbaka a Kasar ta Mali, wanda cikin dan kankanin lokaci hare-haren ya shafi Kasashen Nijar da Burkina faso dake makotaka da ita, duk kuwa da girke dubban sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya.

Harin baya-bayan nan na zuwa ne a yayin da fusatattun yan adawar Mali ke yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar keita matsin lamba ya gaggauta sauka daga karagar mulki, la’akari da matsalolin da suka dabaibaye Kasar kama daga hare haren mayakan jihadi zuwa matsalolin tattalin arziki, da kuma tsananin rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI