Kamaru

Farmakin Boko Haram kan sansanin 'yan gudun hijira ya fusata MDD

Wasu 'yan Najeriya dake gudun hijira a garin Goura dake Kamaru bayan tserewa rikicin Boko Haram a watan Fabarairun 2019
Wasu 'yan Najeriya dake gudun hijira a garin Goura dake Kamaru bayan tserewa rikicin Boko Haram a watan Fabarairun 2019 © UNHCR/Xavier Bourgois

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kaduwa gami da fusata da kazamin harin da aka kai kan sansanin ‘yan gudun hijirar dake arewacin kasar Kamaru wanda yayi sanadiyar hallaka mutane 18.

Talla

Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta Majlisar ta bayyana cewar maharan sun yi amfani da na’ura mai fashewa ne da ake kyautata zaton gurneti ne wajen kai hari sansanin mai dauke da mutane 800 lokacin da suke bacci.

Majalisar tace wasu mazauna sansanin sama da 1,500 da suka kadu sakamakon harin sun tsere zuwa garin Mozogo domin samun mafaka, yayin da Hukumar ta tura ma’aikatan gaggawa domin kula da su.

Hukumar tace an samu akalla hare haren mayakan book haram 87 kusa da iyakar Najeriya da Kamaru daga watan Janairu zuwa yanzu.

Mahamat Chettima Abba, Magajin Garin dake kula da Yankin yace babu tantama mayakan book haram ne suka jefa gurnetin, yayin da ma’aikatar cikin gidan Kamaru tace basu iya tantance kungiyar da ta kai harin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI