Ambaliyar ruwa ta shafi mutane dubu 50 a Sudan - MDD
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya tace ambaliyar ruwan bana ta shafi akalla mutane sama da 50,000 a kasar Sudan a cikin mako guda da ya gabata.
Kungiyar Jinkai ta Majalisar OCHA tace ruwan saman da ake ta shatatawa a cikin mako guda a sassan kasar ta Sudan ya haifar da ambaliya da zabtarewar kasa da rushewar gidaje da kayan more rayuwa a akalla Jihohi 14 daga cikin 18 dake cikin kasar.
Ministan cikin gida Eltrafi Elsidik yace akalla mutane 5 suka mutu sakamakon ambaliyar, yayin da sama da gidaje 3,500 suka rushe.
Jami’in kungiyar OCHA a Sudan Saviano Abreu, yace a shekarar 2019 mutane sama da 400,000 ambaliya ta shafa a cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu