Mali

UNESCO ta kaddamar da shirin kare al'adun Bandiagara dake Mali

Gine-ginen gargajiya a garin Bandiagara na kabilar Dogon dake yankin tsakiya Mali
Gine-ginen gargajiya a garin Bandiagara na kabilar Dogon dake yankin tsakiya Mali AFP / FRANCOIS XAVIER MARIT

Hukumar bunkasa Ilimi, kimiya da tattalin al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta kaddamar da gagarumin shirin sake gina wasu cibiyoyi dake tattare da al’adu na Bandiagara da ke tsakiyar kasar Mali, wadanda rikici da kuma hare-hare ‘yan ta’adda suka lalata.

Talla

A sanarwar da ta fitar a jiya talata, hukumar ta UNESCO ta ce ta ware kudi dala milyan daya domin sake gina wuraren tarihin da aka lalata.

Har ila yau a karkashin wannan shiri, hukumar za ta yi kokarin ceto sauran muhimman wurare da kuma kayayyakin dake fuskantar barazanar bacewa sakamakon tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin dake tsakiyar kasar ta Mali.

Yankin Bandiagara na kabilar Dogon, na cikin lardin Mopti ne, wanda daga shekara ta 2012 zuwa yanzu ya fuskanci hare-haren ‘yan ta’adda da dama tare da lalata muhimman wuraren tarihi a garuruwa akalla 30 kamar yadda hukumar ta UNESCO ta sanar.

Wasu daga cikin muhimman abubuwan da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin karewa, sun hada da makarbatun da aka killace daruruwan shekaru, sai tufafin gargajiya da ake amfani da su lokacin jana’iza da kuma kwalkwalin fuska da kabilar ta Dogon ta shahra a fagen sassakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.