'Yan tawayen Congo sun kashe fararen hula sama da 1000 cikin wata 6

Wani sojan Ruwanda a Congo
Wani sojan Ruwanda a Congo LIONEL HEALING / AFP

Majalisar Dinkin Duniya tace kungiyoyin Yan bindiga a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun yi sanadiyar kashe fararen hula sama da 1,300 a watanni 6 na farkon wannan shekara, adadin da ya rubanya wadanda aka kashe bara har sau 3.

Talla

Rahotan Majalisar yace tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin bana, mayaka daga kungiyoyi daban daban dake dauke da makamai sun aikata kisan gillar da ya kai akalla 1,315, kuma daga cikin wannan adadi 267 mata ne, yayin da 165 yara ne kanana.

Rahotan da Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar ta rubuta yace a shekarar da ta gabata, mutanen da aka kashe a cikin watanni 6 na farkon shekarar 2019 sun kai 416, sabanin abinda aka gani a bana.

Majalisar ta bukaci karfafa matakan tsaro domin kare lafiyar fararen hular dake zama a wadannan yankuna da Yan bindigar ke kai musu hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.