Mali

Jami'an tsaron Mali sun yi amfani da mugun karfi-Amnesty

Wasu daga cikin jami'an tsaron Mali
Wasu daga cikin jami'an tsaron Mali AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES

Kungiyar Amnesty International ta zargi jami’an tsaron gwamnati da hannu wajen amfani da karfin da ya wuce kima da ya kai ga kashe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Mali a watan jiya.

Talla

Wani rahoto da Amnesty International ta fitar ya ce tana da kwararan shaidun da ke tabbatar da abin da ya faru daga majiyoyi da dama kan yadda jami’an tsaron suka kashe masu zanga zangar.

Jami’in kungiyar a yankin Afrika ta Yamma, Ousmane Diallio ya ce bayan barkewar zanga-zangar da kungiyar ‘June 5 Movement’ a karkahsin Imam Mahmoud Dicko ta shirya daga ranar 10 ga watan Yuli domin bukatar ganin shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga kujerarsa, rahotanni sun nuna cewar an kama jagoransu, abin da ya dada zafafa ta.

Kungiyar ta ce wannan ya sa masu zanga-zangar suka yi tattaki zuwa gidan shugaban kotun fasalta kundin tsarin mulki Manassa Danioko, amma jami’an tsaro tare da masu kare lafiyarsa suka tare su, inda suka yi harbi da bindiga, abin da ya kai ga kashe mutane 4.

Ci gaba da arangamar ya haifar da kashe mutane da dama, yayin da 'yan adawar suka ce sun kai 23, kana wasu sama da 150 sun samu raunuka, sabanin adadin da Firaminista Boubou Cisse ya bayar na mutuwar mutane 11 da wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar na mutane 14.

Kungiyar Amnesty ta bukaci gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI