Najeriya-Amurka

Kungiyar al-Qaeda na shirin addabar arewa maso yammacin Najeriya - Amurka

Osama Bin Laden, tsohon shugaban al-Qaeda da Amurka ta kashe.
Osama Bin Laden, tsohon shugaban al-Qaeda da Amurka ta kashe. Reuters

 Amurka ta ce kungiyar Al Qaeda ta fara kafa sansani a Yankin Arewa maso yammacin Najeriya domin samun gurbin da zata gudanar da harkokin ta.

Talla

Kwamandan rundunar sojin Amurka dake kula da Afirka, Janar Dagvin Anderson ya sanar da haka inda yake cewa gwamnatin kasar sa na tintibar Najeriya wajen musayar bayanan asiri da zummar fahimtar abinda Yan ta’addan ke yi.

Jami’in yace wannan na da matukar muhimmanci wajen fuskantar su a Jihar Barno da kuma inda suka fara kutsawa dake Yankin Arewa maso Yammacin Najeriyar.

Janar Anderson yace musayar bayanan asirin ya zama wajibi, kuma Amurka zata cigaba da baiwa Najeriya muhimman bayanan kan abinda kungiyar Yan ta’addan keyi da abinda book haram keyi da kungiyar ISIS dake Yammacin Afirka da kuma Al Qaidar dake kokarin fadada ikon su.

Tun bayan kaddamar da hare haren kungiyar Boko Haram shekaru 10 da suka gabata, kungiyar ta fi mayar da hankali ne a yankin Arewa Maso Gabas da ya kunshi Jihohin Borno da Yobe da Adamawa, yayin da take kai hari jifa jifa zuwa wasu Jihohi daban daban

Kwamandan yace kutsen da wannan kungiyar tayi zuwa Arewa maso Yamma na iya jefa mutanen Jihohin Kano da Katsina da kuma Kaduna cikin hadari.

Janar Anderson ya yaba wa Najeriya kan irin matakan da take dauka wajen yaki da Yan ta’addan, yayin da yake cewa babu wata kasa da za ta yiwa Najeriyar yakin, sai dai taimaka mata.

Hafsan sojin yace sun dade suna taimakawa Najeriya kuma zasu cigaba da haka, a daidai lokacin da ake saran Birtaniya da wasu kasashe suma su bada nasu taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI