Nijar ta yi asarar sama da Dala miliyan 100 a badakalar makamai

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou. SIMON MAINA / AFP

Wani Binciken asiri ya nuna cewar Jamhuriyar Nijar tayi asarar sama da Dala miliyan 100 wajen badakalar cinikin makamai sakamakon almundahana wajen gudanar da aikin kwangila.

Talla

Rahotan binciken da gwamnatin kasar tayi wanda Jaridar Guardian da ake wallafawa aLondon ta samu, yace kasar tayi asarar kudaden da suka kai Dala miliyan 137 a cikin shekaru 8 da suka gabata wajen cinikin makaman.

Binciken da ofishin Sufeto Janar dake kula da makamai ya gudanar yace akasarin makaman da kasar ta saya daga kamfanonin Rasha da Ukraine da China da kuma wasu kasashe ko an kara kudaden su, ko kuma ba’a mikawa kasar ba, ko kuwa an sayo ta bayan gida.

Rahotan yace a wani lokaci a kan cika takardun bogi da kuma gabatar da kamfanonin da basu da kwarewa domin cika sharuddan hukumomi.

Kungiyar dake yaki da laifuffuka da kuma cin hanci da rashawa mai zaman kan ta da ta karbi rahotan binciken tace akwai matsaloli daga cikin cinikin makaman da kudin su ya kai Dala miliyan 320 daga cikin makaman da kasar ta saya na kudin da ya kai Dala miliyan 875.

Daya daga cikin kwangilolin da suka tada jijiyoyin wuya sun hada da cinikin jiragen sama masu saukar ungulu kirar Mi-171 daga Rasha, inda aka kara sama da Dala miliyan 19 da rabi akan kudin su da aka saya zuwa dala miliyan 62.

Rashin ingantattun makamai sun haifar da asarar rayukan sojin Nijar dake yaki da Yan ta’adda a iyakokin kasar da suka hada da book haram da ISIS da kuma Yan bindigar Mali.

Yanzu haka masu gabatar da kara a Nijar na nazari kan wannan badakala kafin zaben da za’ayi a kasar a karshen wannan shekara.

Tuni badakalar ta haifar da zanga zanga da yajin aiki a cikin Nijar duk da alkawarin da gwamnati tayi na kwato kudaden da akayi rub da ciki da su da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI