Afrika-Coronavirus

Adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 sun zarce 40,000 a Ghana

Wata masana'antar kera kayakin kariya daga kamuwa da cuttuka a Ghana
Wata masana'antar kera kayakin kariya daga kamuwa da cuttuka a Ghana REUTERS/Francis Kokoroko

Gwamnatin  kasar Ghana tace adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kama a cikin kasar sun kai 40,097, yayin da 206 daga cikin su sun mutu.

Talla

Ma’aikatar lafiyar kasar tace yau juma’a an samu sabbin mutane 455 da suka harbu da cutar, yayin da aka sallami karin mutane 254 da suka warke, abinda ya kawo adadin wadanda suka warke baki daya zuwa 36,638.

Kasar Ghana na daya daga cikin kasashen da suke sahun gaba a Afirka wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.