Ambaliyar ruwa ta ritsa da mutane da dama a Nijar
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 19 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a sassan Jamhuriyar Nijar, saboda yadda ake shatata ruwan sama, wanda ya shafi gidaje 6,215 ko kuma mutane 53,000.
Daga cikin yankunan da lamarin ya shafa, jihar Damagaram na daga cikin su, inda aka bayyana cewa mutane da dama ne suka fuskanci ambaliyar .
Kungiyoyi da dama ne yanzu haka ke fatan hukumomin kasar za su dau matakan da suka dace don kai dauki cikin gaggawa ga mabukata.
A shekarar da ta gabata dai masana sun yi gargadin cewa za a fuskantar ambaliya a wasu yankunan kasar ta Nijar,tareda fatan ganin gwamnati ta dau matakan da suka dace a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu