India

Mutane sun mutu a India bayan da jirgin saman dake dauke da su ya rikito

Daya daga cikin jiragen sama dake jigilar fasinjoji
Daya daga cikin jiragen sama dake jigilar fasinjoji REUTERS/Toby Melville

Jirgin saman Fasinjan kasar India ya kaucewa titin sauka da tashin jiragen sama,lamarin da ya janyo hadari a yayin da mutane 14 suka mutu wasu 15 suka samu raunika.

Talla

Jirgin na fasinja mai dauke da mutane 190 ya cira ne daga Dubai na Daular larabawa a yayin da hadarin ya auku a lokacin sauka, a filin sauka da tashin jiragen sama na garin Kozhikode dake jihar kerala a kudancin kasar.

Ma’aikatan filin jirgin sun tabatar da cewa jirgin ya kaucewa titin sauka da tashin jirgi ne a dai dai lokacin da ake ruwan sama kama da bakin kwariya.

Ci kin wadanda suka mutu harda matukin jirgin daya kamar yanda mataimakin Gwamna jihar kerala ya tabatar. Ya kuma kara dacewa dayawa wadanda suka tsira sun samu raunuka.

Ma’aikatar zirga zirga jiragen sama tace jirgin ya kaucewa titin ne kusan karshe titin a yayin da yarabu gida biyu.

Gidan talabijin din kasar ya nuno hoton jirgin baa lama wuta, ya kuma ruraito cewa jirgin yanada matsalar giya wajen sauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.