Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Na yanke shawarar sake tsayawa takara-Ouattara

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara. SIA KAMBOU/AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Nura Ado Suleiman
Minti 1

Shugaban Ivory Coast Alassan Ouattara ya sanar da yanke shawarar sake tsayawa takarar zaben shugabancin kasar da zai gudana a 31 ga watan Oktoba.

Talla

A ranar Alhamis ‘yan sanda a Ivory Coast suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa zanga-zangar magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo a birnin Abidjan.

Daruruwan magoya bayan na Gbagbo sun yi dafifi ne a shelkwatar hukumar zabe, inda suka nemi a sanya sunayen tsohon shugaban da na hannun damansa Charles Ble goude da kuma tsohon Firaminista Guilaume Soro, cikin jerin ‘yan takarar da za su fafata a babban zaben kasar ta Ivory Coast da ke tafe.

Sai dai hukumar zaben ta ce ta ki bai wa tsaffin jagororin damar tsayawa takara saboda manyan laifukan da aka tuhume su da aikatawa a kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.