Najeriya

Bankin Duniya zai baiwa Najeriya Dala miliyan 114 domin yaki da annobar COVID-19

Jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji dangane da  Covid 19
Jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji dangane da Covid 19 Amanuel Sileshi / AFP

Bankin Duniya ya amince da shirin baiwa Najeriya Dala miliyan 114 domin taimaka mata yaki da annobar coronavirus wadda ta addabi kasashen duniya yanzu haka.

Talla

Bankin ya bayyana cewar Dala miliyan 100 daga cikin kudin rance ne, yayin da Dala miliyan 14 kuma tallafi ne da za’a rabawa jihohin kasar 36 da kuma gwamnatin tarayya domin sayen magunguna da kayan gwaji da kuma kayayyakin aikin likita.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da cutar tafi illa a nahiyar Afirka, inda ta kama mutane sama da 45,000 ta kuma kashe 930, yayin da kasar ke fuskantar matsalar yin gwaji.

Daraktan Bankin a Najeriya, Shubham Chaudhuri yace Najeriya na kokarin yaki da cutar amma kuma ana bukatar Karin gwaji a matakan jihohi wadanda ke fuskantar matsaloli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.