Afrika

Bincike dangane da mutuwar firsinoni 44 daga cikin mayakan Boko haram a Chadi

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da dakarun Chadi suke tsare da su
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da dakarun Chadi suke tsare da su REUTERS/Moumine Ngarmbassa

Gwamnatin  Chadi tace mummunar yanayi a gidan yarin kasar yayi sanadiyar mutuwar firsinoni 44 daga cikin mayakan boko haram da aka tsare sabanin zargin cewar guba aka saka musu.

Talla

Hukumar kare hakkin Bil Adama ta kasar tace binciken da ta gudanar ya tabbatar mata cewar mummunar yanayin da gidajen yarin ke ciki da kuma zafi da kishin ruwa da yunwar da ta shafi tarin mutanen da aka tsare a cikin daki guda yayi sanadiyar mutuwar firsinonin.

Binciken ya biyo bayan mutuwar mayakan boko haram 44 daga cikin 58 da aka tsare a tsakiyar watan Afrilu a gidan yarin dake karkashin kulawar jami’an tsaron Jandarmeri bayan an kama su a yankin Tafkin Chadi.

Babban Mai Gabatar da karar kasar ya bayyana gudanar da bincike kan lamarin, bayan da ministan shari’ar Chadi Djimet Arabi yace wata kila mayakan sun kashe kan su da kan su ne wajen shan guba.

Mutuwar mutanen 44 ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Chadi, inda ake zargin gwamnati da hallaka mayakan ba tare da an gurfanar da su a gaban shari’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.