Mu Zagaya Duniya

Kasashen Duniya na shirin kai dauki ga yan Lebanon

Sauti 20:11
Wani soji kasar Lebanon a birnin Beirut bayan fashewar da ta wakana ranar talata
Wani soji kasar Lebanon a birnin Beirut bayan fashewar da ta wakana ranar talata Thibault Camus/Pool via REUTERS

Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya kai ziyarar aiki a yau asabar a kasar Lebanon domin jajanta wa al’ummar da ke alhinin mutuwar sama da mutane 150 sanadiyyar wannan fashewa da ta faru a ranar talatar da gabata.A lokacin wannan ziyara, shugaban na majalisar turai ya gana da shugaba Michel Aoun, da shugaban majalisar dokoki Nabih Berri sannan da firaminista Hassan Diab.A cikin shirin mu zagaya Duniya zaku ji halin da ake ciki a wasu kasashen Duniya  tareda Garba Aliyu Zaria.